23 Janairu 2017 - 10:30
Iran Ta Jaddada Cewa: Zaman Tattaunawa Ne Kadai Zai Warware Rikicin Kasashen Duniya

Mai bada shawara kan harkokin al'adu ga shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zaman tattaunawa da kyakkyawar mu'amala sune hanyar kawo karshen duk wani riciki da tashe-tashen hankula da suke faruwa a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

A jawabinsa a bude zaman taron tattaunawa tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Larabawa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a ranar Asabar da ta gabata: Hassam Din Ashnah ya jaddada bukatar bude kofar zaman tattaunawa a tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Larabawa; Yana mai jaddada cewar kasashen musulmi suna bukatar hadin kai da bunkasar harkokin tattalin arziki da nufin kyautata rayuwar bil-Adama.

A jawabinsa da ya gabatar a zaman taron; wakilin kasar Iraki Jawad Aziz Almusawi ya jaddada cewa: Masana da manazarta suna da gagarumar rawar da zasu taka a fagen wayar da kan al'umma a kasashensu, sannan bude kafar tattaunawa a tsakanin kasashe musamman tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran kasashen Larabawa zai taimaka wajen farfado da bunkasa da ci gaban al'adu, tattalin arziki da ilimi a tsakanin al'ummun yankin.

A nashi bangaren Abdur-Rahman Al-Audha manazarci dan kasar Oman ya bayyana cewa: Bude zaman tattaunawa a tsakanin kasashen Larabawa da jamhuriyar Musulunci ta Iran zai kara karfafa tushen addinin Musulunci ne tare da yaduwar koyarwarsa a duniya. 288